Matakan da kasar Amurka ta dauka na cire wasu jerin takunkuman karayar tattalin ariziki da ta saka kan kasar Iran abu ne mai kyau, sai dai ba su wadatarwa, in ji ministan harakokin wajen Iran. Bayan da Amurka ta bayyana soke wasu jerin takunkumai da ta saka wa kasar, da ke da alaka da aikin samar da makamashin nukliyar da kasar ta Iran ke yi.
Matakin da gwamnatin Joe Biden ta dauka ya kasance mai mahimmanci ga mahukumtan Téhéran a dai dai wannan lokaci da a birnin Vienne, a ke ci gaba da tattaunawar yinkurin ceto yarjejeniyar 2015 kan aikin Nukliyar da ke kan ganiyar karshe.
A 2018 ne, shugaban Amruka da ya gabata Donald Trump, ya janye kasarsa daga cikin yarjejeniyar tare da maida daukacin takunkuman kariyar tattalin arizikin da Amrukar ta kakabawa kasar ta Iran, al’amarin da ya sa, Iran jingene aiki da wasu fannoni na yarjejeniyar kawo yanzu da gwamnatin shugaba Biden, ta sake maido kasar kan teburin tattaunawar neman ceto tsohuwar yarjejeniyar ta 2015 amma tare da kwaskwarima. Matakin da Iran ta ce ba ta yarda da shi ba.
A wani labarin na daban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki manyan kasashen duniya, inda ya ce sun aikata babban laifi saboda yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu. Kalamansa na zuwa ne bayan fitar da wani sabon rahoto kan illolin sauyin yanayi, inda ya zargi manyan kasashen da ta’azzara matsalar.
Sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce, babban abin tashin hankalin da wannan sabon rahoton kwararrun ya kunsa, shi ne yadda matsalar ta sauyin yanayi ta yi wa rayuwar bil’adama illa.
Rahoton ya kuma bukaci tuhumar wadannan manyan kasashe na duniya saboda yadda suka gaza wajen daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar.
Mista Guterres ya bayyana cewa, kusan rabin al’ummar duniya na rayuwa cikin gagarumar barazana a yanzu, yayin da sukurkucewar alaka tsakanin halittu da muhalli ta kai matakin kololuwa a cewarsa.
Magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa, babu yadda za a karyata batun cewa, lallai hayaki mai gurbata muhalli shi ne ummul-haba-i-sin sauyin yanayin.
Sannan ya ce, watsi da nauyin da ya rataya akan shugabannni na matsayin babban laifi, kuma manyan kasashen duniyar da suka fi gurbata muhalliu, su ne da laifin cin amanar doran duniyar da muke rayuwa a ciki a cewarsa.
An dai fitar da rahoton kwararrun ne na Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da rikcin Rasha da Ukraine ke daukar hanklulan kasashen duniya.