Iran Na Maraba Da Fadada Dangantaka Da Kasashen Yankin Musamman Na Tekun Kasfiya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdollahiyan ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Turkuminstan Rashid Muradov inda ya taya shi murnar fara Azumin watan ramadan, tare da tattauna dangane da muhimman batutuwa da suka shafi kasashen biyu na kasa da kasa musamman batun kara fadada hadin guiwa tsakanin kasashen yankin na kasfiya.
Da yake bayani game da batun shirya dafatarin yin aiki tare a mashigar tekun kasfiya a bangaren kimiyya, bincike da ayyukan ceto, da yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma fada hadin guwai tsakanin kasahen yankin, Moradov ya bada shawara a gudanar da taron tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen guda biya na mashigar tekun kasfiya domin fadada hanyoyin yin hadin guiwa tsakanin bangarorin biyu.
READ MORE : HKI; Mun Sami Koma Baya Wajen Yadda Jiragenmu A Saman Kasar Lebanon Cikin ‘Yanci.
A nasa bangaren ministan wajen kasar iran ya cewa A kowanne lokaci Iran tana maraba da duk wani mataki na fada dangantaka tsakanin musamman a mashigar tekun kasfiya, daga karshe ya taya takwaransa na kasar Turkumanistan farin cikin shiga Azumin wata Ramadana mai alfarma.
READ MORE : Red Cross; Miliyoyin Mutane Suna Fuskantar Yunwa A Nahiyar Afica.