Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa Firaministan India Narendra Modi sun cimma jituwa kan kudirin aiki tare a yankin Pacific, sabuwar alakar da ke kulluwa bayan takaddamar kwangilar jirgin ruwan yakin karkashin teku tsakanin Faransar da Australia.
A zantawarsu ta wayar tarho yau talata, shugabannin biyu sun amince sun karfafa alakarsu ta fuskar kere-kere da kimiyya da kuma tsaro baya ga kasuwanci.
Yayin zantawar ta su Macron ya roki Narendra Modi kan rike amanar juna don kaucewa matsalar da Faransar ta samu a baya-bayan nan da Australia.
Emmanuel Macron ya sha alwashin kyautata sabon kwancen tsakanin kasar ta Turai da India daga gabashin Asiya a wani yunkuri na karfafa kasancewarsu a yankin na Pacific da manyan kasashe ke ci gaba da girke jirage da makamai.
Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen ta ce sam ba a yi wa Faransa adalci ba, a batun cinikayyar jirgin ruwan karkashin teku da ta kulla da Australia, tana mai jadadda cewa hakan tamkar cin amana ne.
Tun makon da ya gabata ne, cacar-baka ta barke tsakanin Faransa da Amurka sakamakon yadda Faransar ke zargin Amurka da yi mata kutungwila wajen kwace cinikayyar jirgin karkashin tekun.
A cewar Ursula Von der Leyen Tarayyar Turai ba za ta amince a yi wa wata mambarta makamancin wannan cin mutunci ba.
Tun da fari dai Faransa ce ta kulla yarjejeniya da kasar Australia wajen sayar mata da jirgin ruwan karkashin teku, amma kwatsam sai labarin janye yarjejeniyar ya bulla.
Australia ta sanar da janye yarjejeniyar da ta kulla da Faransa, bayan da tuni Faransan ma ta fara aikin samar da jirgin, abinda ta ce ba mai sabuwa ba ne.
Bayan da Australia ta janye yarjejeniyar ta kuma kulla makamanciyar ta da Amurka, abin da tarayyar Turai ta ce karara cin dunduniyar Faransa ne da kuma yi mata zagon kasa.
Sai dai tuni shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bukaci tattaunawa da na Faransa don shawo kan lamarin, da ka iya wargaza alakar su.