IAEA; Rasha ta hana ‘ma’aikatan tashar nukiliya ta Chernobyl hutu’.
Shugaban hukumar da ke kula da yaduwar makamashin nukiliya ta duniya, IAEA ta yi kira ga sojojin Rasha da ke iko da tashar nukiliya ta Chernobyl da ke arewacin Ukraine, da suk kyale wasu ma’aikatan tashar su huta.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, Rafael Grossi ya ce jami’an gwamnatin Ukraine sun sanar da shi cewa har yanzu ma’aikatan tashar 210 ne ke aiki n atsawon mako biyu babu hutawa.
Grossi ya ce ya damu matuka ga halin da suke ciki da kuma cewa suna iya fadawa cikin halin matsanancin damuwa.
Ya kuma ce ya dace ma’aikatan su rika hutawa kuma a rika sauya su da wasu ma’aikatan, inda ya ce hutu na da muhimmanci ga kasancewar komai na aiki lafiya.
Sojojin Rasha sun kutsa cikin tashar nukiliyar – wadda ita ce tashar da aka yi hatsarin nukiliya mafi muni a duniya – hatsarin da ya auku a ranar 24 ga watan Fabrairun 1986.
Grossi ya kuma ce hukumar ta daina samun bayanan halin da na’urorin tashar ke ciki, bayanan da a baya suke iya samu ta intanet.
READ MORE : Shugaban Turkiyya Erdogan na fatan sasanta Rasha da Ukraine.