HKI; Mun Sami Koma Baya Wajen Yadda Jiragenmu A Saman Kasar Lebanon Cikin ‘Yanci.
Kwamandan sojan saman HKI ya bayyana cewa; “Yancin da jiragen saman Isra’ila na yaki suke da shi na yin shawagi a samaniyar kasar Lebanon, ya sami koma baya.
Kafafen watsa labarun HKI ne su ka ambato janar Amikam Nurkin wanda bai dade da yin murabus ba, a hira da mai sharhi akan harkokin soja na HKI Royi Sharon yana fadin cewa; Ashekarar da ta gabata Hizbullah ta harba makami mai linzami akan jirgin sama maras matuki, kuma saura kiris ya same shi. Hakan ya sa a Isra’ila an fahimci cewa abubuwan mamakin da Hizbullah ya boye saboda yaki mai zuwa sun fara bayyana”
Har ila yau ya kara da cewa; Jiragen da Isra’ila take turawa zuwa saman Lebanon domin tattaro bayanai da daukar hotuna, sun wayi gari suna fuskantar barazar harbi daga makamai masu linzami na Hizbullah”
READ MORE : ICC Tana Son Ganin An Kitse Batun Shari’ar Darfur Dake Gabanta.
Shi kuwa Nurkin ya ci gaba da cewa; Abinda hakan yake nufi shi ne cewa a yanzu muna da karancin bayanai na leken asiri.”
READ MORE : Rasha Ta Kori jami’an Diflomasiyyar Jamus 2 Saboda Hukuncin Kotun Berlin.