Mataimakin Firaministan kasar Ukraine Iryna Vereshchuk, ya ce harin da Rasha ke kaiwa kan Mariupol ya hana aikin kwashe ‘yan gudun hijira daga birnin mai tashar jiragen ruwa na Ukraine.
Bayanai sun ce sojojin Rasha da suka dakatar da wasu motocin bas na mutanen da ke kokarin tserewa daga yankin Kyiv, sun yi wa birnin Mariupol kawanya.
Kawo yanzu fararen hula dubu 1 da 582 suka rasa rayukansu a Ukraine tun bayan harin da Rasha ta kai kan kasar.
A wani labarin na daban Shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince da shirin aiki da mayakan sa kai, ciki har da na kasashen waje don yakin Ukraine, inda ya aike da dubban dakarun kasarsa a wani abin da ya kira rawar soji ta musamman.
A cewar Shoigu, fiye da ‘yan sa kai dubu 16, akasarinsu daga gabas ta tsakiya ne suka mika bukatar shiga wannan yki da ake yi a Ukrine.
A kan batun makaman da aka samar daga yammacin Turai, wadanda akasarinsu suka shiga hannun sojojin Rasha, Putin ya ce, mika su ga bangaren sojin ‘yan awaren gabashin Ukraine.
Putin ya kuma umurci ministan tsaron, Shoigu da ya shirya wani rahoto na musamman a kan yadda zaa karfafa tsaron iyakokin rasha da yammacin Turai, duba da matakin da kungiyar tsaro ta NATO ke yunkurin dauka daga baangaren.