Gwamnatin Birtaniya ta sanar da amincewa da shirin hamshakin attajirin Amurka Todd Boehly na sayen kungiyar Chelsea daga hannun takwaransa na Rasha Roman Abramovich da aka laftawa takunkumi.
A farkon watan Maris ne dai Abramovich ya saka Chelsea a kasuwa, kafin gwamnatin Burtaniya ta lafta masa takunkumi sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, sai dai an yi ta jan kafa wajen kammala cinikayyar saida kungiyar ta Chelsea, sakamakon yadda gwamnatin Birtaniya ba ta son attajirin na Rasha ya amfana da riba daga cinikin.
Abramovich, wanda ita ma Kungiyar Tarayyar Turai EU ta kakabawa takunkuman zalunci, gwamnatin Birtaniya ta bayyana shi a matsayin makusancin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Sayar da Chelsea mai rike da kofin gasar cin zakarun Turai ta kakar wasan shekarar 2021, ya kawo karshen shekaru 19 na nasarorin da ba ta taba samu ba a karkashin Roman Abramovich mai shekaru 55, wanda ya jagoranci kungiyar wajen lashe kofunan Firimiya biyar da na gasar zakarun Turai biyu.
A wani labarin mai kama da wanna bayanai daga wasu majiyoyi kwarara wadanda kawo yanzu ba a tabbatar ba a hukumance s un ce hamshakin attajirin nan dan kasar Rasha Roman Abramovich ya shiga mawuyacin hali tun bayan da gwamnatin Birtaniya ta kwace kadarorinsa a makwannin baya, sakamakon mamaye Ukraine da kasarsa Rashan ta yi.
Yanzu haka dai rahotanni sun ce, Abramovich na shirin fara tuntubar abokansa attajirai domin samun aron kudi cikin gaggawa.
A halin da ake ciki dai, Abramovich na kokarin sayar da kungiyarsa ta Chelsea, duk da dai babu tabbas kan tsarin da za a bi wajen aiwatar da wannan ciniki, ba tare da gwamnati ta karbe iko da kulob din da ke birnin Landan ba.
A cewar wani rahoto da jaridar Sun ta buga, Abramovich na neman aron zunzurutun kudi kusan fam miliyan daya domin cigaba da biyan wasu hadimansa albashi.