Gungun ‘yan adawar jamhuriyar Africa ta tsakiya sun bayyana janyewar su daga taron sulhuntawa da za’a gudanar a kasar, bayan da aka janye gayyatar da aka yiwa gungun shugabannin ‘yan tawaye.
Jamhuriyar Africa ta tsakiya dai ta fada cikin tashin hankali ne tun shekarar 2013, to amma a makon da ya gabata Shugaban kasar Faustin Archange Touadera ya bukaci tattaunawar sulhu da dukannin masu ruwa da tsaki makkonni 15 da ya shan alwashin yin wannan zama amma ban da ‘yan tawaye.
To amma dakatar da shugabannin gungun ‘yan tawayen kasar daga halartar taron ne ya sanya kakakin gungun ‘yan adawar Nicolas Tiangaye ya sanar da kin halartar ta su a taron da aka shirya gudanar da shi wannan litinin.
Sai dai duk da wannan sanarwa Kakakin gwamnatin kasar Albert Yaloke Mokpeme ya ce za’a gudanar da taron, yana mai cewa shugaban kasar ya yi mamakin janyewar ‘yan adawar daga halartar taron.
Gudanar da taron hadin kan da tabbatar da zaman lafiya na cikin alkawurran da shugaban kasar ya dauka a yayin yakin neman zaben da ya gudanar a bara, a yunkurin sa na mayar da kasar kan wanzajjen zaman lafiya.
A wani labarin na daban kuma Masu binciken hatsarin Jirgin Malaysia Samfurin MH17 da ya kashe mutane kusan 300 sun fito da sakamakon bincikensu na Karshe, inda suka tabbatar da cewa harbo jirgin aka yi daga gabashin Ukraine da Makami mai Linzami BUK da Rasha ke kerawa.
Shugaban Tawagar Masu binciken daga kasar Nerthaland Tjibbe Joustra ya ce mafi yawan tarkacen Jirgin Samfurin MH17 an tsinto su ne a kauyuka da dama da suka hada da Grabove, Rozsypne da Ptropavlivka da ‘yan tawayen ukraine suka fi yawa.
Bincike ya kuma tabbatar da cewar an harba makamin mai linzami ne daga nisa kilomita 320 daga gabashin Ukraine.
Malaysia dai ta sha alwashin shigar da karar wadan da ke da alhakin rikitowar wannan jirgi.
Rasha dai ta bayyana shakun ta dangane da wannan Sakamako.