Gwamnatin Equatorial Guinea ta biya diyya ga iyalai 84 na mutane fiye da 100 da suka mutu sakamakon fashewar bama-bamai a wani sansanin sojin kasar a shekarar bara.
Bayanai sun ce gwamnatin Equatorial Guinea ta ware CFA miliyan 700 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.1 ne don biyan diyya ga wadanda abin ya shafa, inda iyalan wadanda suka mutu suka samu CFA miliyan takwas kowannensu yayin da wadanda suka jikkata suka samu CFA miliyan 4-4.
An yi taron mika diyyar ne a ranakun Juma’a da kuma Asabar karkashin jagorancin Teodoro Nguema Obiang Mangue, mataimakin shugaban kasa kuma dan shugaban kasar da ya dade yana mulki.
A wani labarin na daban kuma Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya a Libya mai fama da rikici ta yi tayin shiga tsakani don sansanta rikicin siyasar da ya kunno kai tsakanin bangarorin biyu a kasar, bayan da aka samu kafuwar gwamnatoci guda 2 da suka fara gudanar da mulki a baya bayan nan.
Cikin wasu jerin sakwanni da ta wallafa a shafinta na Twitter, Williams wadda take mashawarciya ta musamman ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres kan kasar Libya, ta yi gargadin cewa kafa gwamnatoci biyu masu adawa da juna ba shi ne matakin da zai warware matsalar kasar ba.
Jami’ar ta bukaci Majalisar Wakilai da ke gabashin kasar da kuma Majalisar zartaswa mai hedikwata a birnin Tripoli, da su zabi wakilai shida kowannen su, don kafa kwamitin hadin gwiwa domin samar da matsaya kan sansanta rikicin siyasar da ka iya kazancewa.