Guguwar Eunice ta kashe akalla mutane tara a Turai, kamar yadda wasu alkalumma suka nuna a ranar Juma’ar nan.
A birnin London ‘yan sanda sun ce wata mata ‘yar shekara 30 ta mutu bayan da wata bishiya ta fada kan wata mota da take fasinja a ciki. Shi kuma wani mutum a arewa maso yammacin Ingila ya rasa ransa ne bayan da tarkacen gine-gine ya afkawa gilasan motar da yake tafiya a ciki.
A Netherlands mutane 3 suka mutu sakamakon fada musu da bishiya ta yi, sai kuma wani mutum a gabashin Ireland, yayin da wani dan kasar Canada mai shekaru 79 ya mutu a Belgium.
Wani direban mota kuwa ya mutu ne a lokacin da motarsu ta yi karo da wata bishiya da ta fada kan wata hanya kusa da Adorp a lardin Groningen da ke arewacin Netherlands.
A Jamus kuma, wani direban mota ya mutu bayan da wata bishiya ta buge motarsa a kusa da garin Altenberge.
A wani labarin na daban Wata kakkarfar guguwa da masana suka lakabawa suna Bella ta katse layukan lantarkin akalla gidaje dubu 18 a yankunan Normandy da Brittany dake arewacin kasar Faransa.
A yankunan gabashi da tsakiyar Faransa kuwa guguwar ta Bella ta katse lantarkin wasu gidajen kimanin dubu 34.
Ma’aikatar lura da yanayin kasar tace guguwar ta Bella na tsala gudun kilomita 100 zuwa 120 a lokacin da ta afkawa.
Rahotanni sun ce akalla mutane 11 suka mutu sakamakon iftila’in guguwar, yayinda wasu dadama suka bace.