FIFA ta bukaci hukumar kwallon kafar Rasha ta doka wasannin da suka rage mata na nema gurbi a gasar cin kofin Duniya ba tare da tutar kasa ko kuma taken kasa koma sunan Rasha a tare da su ba, saboda yadda kasar ke yi wa Ukraine mamaya
Rasha dai na bukatar doka wasan cike gurbi tsakaninta da Poland cikin watan Maris mai kamawa a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya.
Sai dai tuni wasu kasashe ciki har da Poland da kuma Sweden suka yi watsi na wannan mataki na FIFA ko da ya ke ita kanta hukumar wasannin ta Rasha ba ta sanar da aminta da matakin ba.
A bangare guda tuni hukumar kwallon kafar Ingila ta sanyawa tawagar kwallon kafarta haramci din-din-din game da doka kowanne nau’in wasa a kowanne mataki tsakaninta da Rasha saboda abin da ta kira mamayar da kasar ke yiwa Ukraine.
Sanarar da hukumar kwallon kafar ta fitar ta ce haramcin zai shafi hatta wasannin nan gaba koda al’amura sun nutsa tsakanin Rashan da kasashen Duniya.