Bayan da aka jingine shirin sake fasalta binciken takardun jama’a da ‘yan sandan kasar ne, a shekaran jiya, wani gungun kungiyoyin kare hakkin dan adam a Faransa, sun yanke shawarar tunkarar babbar kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar, domin tilastawa gwamnatin, dakatar da cin zarafin mutane da nuna wariya da ‘yan sanda ke yi.
Shi dai korafi da aka shigar gaban kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta Faransa, wani gungun kungiyoyin kare hakkin dan adam su 6 ne suka tinkari kotu da shi, wadanda suka hada da kungiyar Amnesty International da kuma Human Rights Watch, ya faro ne tun cikin watan Janairun da ya gabata.
A baya dai, kungiyoyin sun bukaci gwamnatin Faransa, ta samar da wasu jerin sauye-sauye, ga aikin na ‘yan Sanda, wajen daukar kwararan matakai domin kawo karshen binciken cin zarafin da ‘yan sanda takardun na wulakanci da nuna wariya da ‘yan sanda ke yi wa al’umma a kasar, inda aka baiwa mahukumtan na Faransa wa’adin watanni 4 su bada amsa kan bukatar kungiyoyi.
To a yayin da yanzu haka wa’adin watanni 4 da aka bai wa gwamnatin domin bada amsa kan korafin ke cika ba tare da ta ce uffan ba, kungiyoyin kare hakkin dan adam din sun tsallaka a mataki na gaba, inda suka shigar da karar gwamnati a gaban kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta Faransa kan batun domin tilastawa gwamnatin samar da maslaha kan korafin.
A faransa dai ana fama da matsaloli da suka hada da na tattalin arziki gami da matsin rayuwa wanda ya sanya tsananin fusata daga bangaren mutanen kasar a yayin da gwamnatin kasar ke cikin halin tsaka mai wuya sakamakon karyewar tattalin arzikin kasar bisa dalilan da suka hada da bullar annobar korona wacce ta karya tattalin arzikin kusan gabadayan kasashen nahiyar yammacin turai, lamarin dake zaman babbar barazana ga kasashen.