Gwamnatin Chadi ta ce, fada da aka gwabza tsakanin masu hakar zinari a arewacin kasar ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, da kuma jikkata wasu da ba a san adadinsu ba, a yayin da wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ka ce adadin wadanda suka mutu a rikicin ya kai kusan mutane 200.
A wata sanarwa da ministan yada labaran kasar, Abderaman Koulamallah ya fitar, ta ce fada da aka yi a Kouri Bougoudi a ranar litinin ya haifar da tashin hankali tsakanin Larabawa daga kan iyakar Libya da ‘yan kabilar Tama, wadanda suka fito daga gabashin Chadi.
Sakamakon haka ya haifar da asarar rayukan mutane da kuma jikkata da dama.
Shugaban jam’iyyar adawa ta Transformers, Succes Masra, ya wallafa a shafin Facebook inda ya ce akalla mutane 200 ne suka mutu.
Babbar kungiyar ‘yan tawayen FACT da kuma shugaban kwamitin kare hakkin bil’adama na kasar, Mahamat Nour Ibedou, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa adadin wadanda suka mutu ya kai akalla 200, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.
Yankin iyakar Kouri Bougoudi, mai tazarar sama da kilomita 1,000 daga arewa maso gabashin babban birnin kasar N’Djamena, na cikin yankin hamadar Tibesti mai tsaunuka, wanda ba a iya samun hanyar sadarwa ta tarho.
Gwamnati ta aike da karin jami’an tsaro,tareda rakiyar wasu wakilan ta da suka hada da ministan tsaron kasar ta Chadi.