Shugaban Turkiyya Recep Tayyio Erdogan ya yi kira ga Isra’ila da ta dakata da harin da take kaiwa a Gaza da kuma “daina rashin hankalin da take yi,” a yayin da take kara zafafa hare-hare da ta kai a cikin dare.
“Karin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza ya kara fadawa kan mata da yara da farar hula da ba su ji ba su gani ba, lamarin da ya kara munana rikicin,” in ji Erdogan a sakon da ya wallafa a shafinsa na X.
Shugaban kasar ya bukaci jama’ar kasarsa da su halarci babban gangamin da za a yi a ranar Asabar a filin jirgin sama na Ataturk a ranar Asabar domin nuna goyon baya ga mutanen Falasdinu.
Ana sa ran shugaban zai yi jawabi ga taron jama’a a wurin. An soma wannan rikicin ne tun a ranar 7 ga watan Oktoba bayan kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kaddamar da shirin Operation Al Aqsa Flood – wanda wani hari ne na ba-zata da ya kunshi harba rokoki da kuma kutsawa cikin Isra’ila ta sama da kasa da kan tudu.
Hamas ta ce ta yi haka ne domin mayar da martani kan shiga Masallacin Al Aqsa da dakarun Isra’ila suka yi da kuma yadda Yahudawa ‘yan kama wuri zauna ke ci gaba da kai farmaki ga Falasdinawa.
Daga nan ne sojojin Isra’ila suka kaddamar da hari ba kakkautawa a cikin Gaza. Harin ya kara kazanta a ranar Juma’a da dare bayan sojojin sun bayyana cewa sun fadada ayyukan da suke yi ta sama da kasa a Gaza.
Isra’ilar ta kuma katse intanet da sauran kafofin sadarwa a yankin da ta mamaye. Akalla Falasdinawa 7,326 Isra’ila ta kashe tun bayan da ta soma kai hare-hare.
Kashi 70 na wadanda Isra’ilar ta kashe a Gaza mata ne da yara, kamar yadda alkaluman hukumomi suka tabbatar.
A Isra’ila kuwa, adadin mutanen da suka mutu ya kai sama da 1,400.
Mutum miliyan 2.3 da ke zaune a Gaza na fama da karancin abinci da ruwa da magunguna sakamakon irin hare-hare ta sama da Isra’ila ke kaiwa.
Source: TRTAFRICA