Shugaba Bola Tinubu ya taya shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, murnar lashe zaben da ya sake yi.
Tinubu, wanda ya yi amfani da shafinsa na Twitter a karon farko a matsayin shugaban Nijeriya a ranar Litinin, ya ce nasarar zabe alama ce da ke nuna cewa Erdogan ya ci gaba da rike cikakkiyar amanar al’ummar Turkiyya.
Tunibun ya kara da cewa yana fatan samun hadin kai tsakanin Nijeriya da Turkiyya.
Tinubu ya rubuta cewa: “Ina taya Shugaba Recep Tayyip Erdoğan (@RTERdogan) murnar nasarar zaben da ya yi a baya-bayan nan, nasarar zaben wata alama ce da ke nuna cewa ya ci gaba da rike cikakkiyar amana da amincewar al’ummar Turkiyya.
“Ina yi masa fatan samun nasarar wa’adin mulki tare da fatan samun hadin guiwa tsakanin kasashenmu biyu.”
A wani labarin na daban yau Talata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya fara aikinsa a fadar shugaban kasa, lamarin da ke nuni da cewa wa’adinsa ya fara aiki.
Tawagar shugaban kasar ta isa fadar gwamnatin tarayya da misalin karfe 2:35 na yammacin ranar Talata.
Da isowarsa, shugaba Tinubu ya dan dakata a kofar shiga domin duba jami’an tsaro, inda ya tattauna da su kafin ya shiga cikin fadar gwamnatin.
Fitattun mutanen da suka halarci tarbar shugaban kasar sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele; Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) Mele Kyari, da Dele Alake da James Faleke.