Abin da muka sa a gaba a halin yanzu shi ne samar da tsagaita bude wuta, kuma bayan haka, za mu yi kokarin sanya gwamnatin Isra’ila ta biya diyyar laifukan da ta aikata a Gaza. Erdogan
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya nakalto maku daga tashar labarai ta -IRNA- cewa Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana cewa: Isra’ila gwamnatin ta’addanci ce kuma mutumin da ke mulkinta ya sa Isra’ilawa suka yi masa tawaye kuma karshen mulkinsa (Binyamin Netanyahu) ya kusa.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, Rajab Tayyib Erdogan ya ce: Idan Jamus ta yi kokarin shiga tsakani don ganin an sako fursunonin Palastinawa 10,000 a yankunan da aka mamaye, kasar a shirye take ta yi kokarin kubutar da ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza. .
Ya kara da cewa: Dole ne Isra’ila ta saki fursunonin Palasdinawa, ta yadda bayan haka, Turkiyya za ta yi amfani da kokarinta na sako fursunonin daga hannun Hamas.
Ya fadi hakan ne yayin da yake a cikin jirgin sama yana mai dawowa daga ziyarar aiki a Jamus, shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Wajibi ne a sako fursunonin Palasdinawa da farko, ta yadda Hamas ma za ta sako fursunonin Isra’ila.
Erdoğan ya jaddada cewa: Lokacin da wadanda suka mutu a arangama suka zamo musulmi ne to kasashen yamma ba sa nuna damu da su. Me yasa kasashen Yamma suka yi shiru game da shahadantar mutane dubu 13 da gwamnatin Isra’ila ta yi?
Shugaban na Turkiyya ya bayyana cewa: Za mu yi kokarin gurfanar da Isra’ila kan laifukan da ta aikata a Gaza ta hanyar amfani da kwararrun lauyoyi kusan 200.
Erdoğan ya yi nuni da cewa, Isra’ila ta kai hari Gaza tare da kashe fararen hula cikin rashin tausayi, kuma dalilin hakan ba wai karfin wannan gwamnatin ba ne, illa dai gazawar makwabtanta.
A yayin da yake sukar matsayar kasashen musulmi dangane da zaluncin gwamnatin sahyoniyawan a Gaza, shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa: Ayyukan Isra’ila a Gaza laifi ne na yaki.
A karshe Erdogan ya ce: Abin da muka sa a gaba a halin yanzu shi ne samar da tsagaita bude wuta, kuma bayan haka, za mu yi kokarin sanya gwamnatin Isra’ila ta biya diyyar laifukan da ta aikata a Gaza.
Source: ABNAHAUSA