Kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO ta jaddada takunkuman da ta lafta wa gwamnatin mulkin sojin Mali bisa jinkirta mayar da mulki ga hannun farar hula da ta yi.
ECOWAS ta bukaci jagororin gwamnatin sojin Guinea da su gabatar da jadawali karbabe na mika mulki ga fara hula a karshen watan Afrilu, ko kuma su fuskanci takunkumai.
A wata sanarwa, ECOWAS din ta ja kunnen sojojin da ke mulkin Burkina Faso da cewa idan ba su saki tsohon shugaba Roch Marc Christian Kabore da suka wa daurin talala ba zuwa Alhamis na mako mai zuwa, za a kakaba musu takunkumi.
Taron da aka yi a birnin Accra na Ghana na zuwa ne watanni 3 bayan da kungiyar ta ECOWAS ta kakaba wa Mali takunkumai.
A wani labari na daban Yayin da zaben shekarar 2023 ke kara karatowa a Najeriya, Babbar Jam’iyyar adawar kasar ta PDP na cigaba da fuskantar matsalolin cikin gida inda wasu daga cikin jiga jigan ‘yayan ta ke ficewa suna komawa Jam’iyyar APC mai mulki.
Rahotanni sun ce Ayade ya bayyana sauya shekar ne bayan ganawar da yayi da wasu takwarorin sa a birnin Calabar da suka kunshi shugaban Gwamnonin kasar Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da shugaban Gwamnonin Arewa Simon Lalong da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma da kuma takwaran san a Jigawa Abubakar Badaru tare da shugaban Jam’iyyar na riko Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe.
Wannan na zuwa ne bayan sauya shekara da Gwamnan Ebonyi David Umahi yayi daga PDP zuwa APC, yayion da takwaran sa na Edo Godwin Obaseki ya bar APC zuwa PDP lokacin da ta hana shi tsayawa takarar wa’adi na biyu.