Dubban mutane ne suka isa Jamhuriyar Nijar bayan da suka tsere wa rikici da ake yi tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin Mali, kamar yadda wani rahoton majalisar dinkin duniya ya bayyana a jiya Juma’a.
Ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya ya ce dubban mutane sama da fararen hula 400 ne aka yi amannar sun mutu sakamakon rikicin na kungiyoyi masu dauke da makamai.
Wasu daga cikin ‘yan gudun hjirar na karbar taimako daga hukumar abinci ta duniya.
A wani labarin na daban A Asabar din nan Ukraine ta ce dakarun Rasha sun fara barin yankunan arewacin kasar a kusa da iyaka da babba birnin kasar Kyiv da birnin Chernigiv, a yayin da kungiyar agaji ta Red Cross suke wani shirin fara kwashe fararen huka daga birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa.
Ukraine ta ce dakarun Rash ana mayar da hankali ne a yankunan kudanci da arewacin kasar, kwana guda bayan da dubban mutane suka samu ficewa daga Mariupol da saurn yankuna a cikin ayarin motocin bas bas da sauran motoci.
Wani mai bai wa shugaban kasar Ukraine shawara Mykhaylo Podolyak ya ce Rasha ta mayar da hankali a kan wani sabon salo ne a mamayarta yanzu.
Ya ce a yayin da alamu ke nuna dakarun Rasha na ficewa daga biranen Kyiv da Cherngiv, aniyarsu dai ita ce su karbe cikakken iko da yankunan da suka mamaye, don su zauna su kara karfi.
Podolyak ya ce lallai dakarun Ukraine za su bi su yanunan, su kuma kafa tsarin tsaron sama, kuma su kasance masu iko a wurin.
Mariupol ya kasance wani mahimmi birni na Ukraine da ya sha luguden wuta daga Rasha, inda rhotanni ke cewa an kashe mazauna yankin dubu 5.