An rantsar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba a matsayin sabon shugaban Burkina Faso, bayan wasu ‘yan makwanni da ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kabore.
A wani biki da aka watsa ta kafar talabijin, Damiba ya sha rantsuwar kama aiki a gaban babban kwamitin fasalta kundin tsarin mulkin Burkina Faso, inda ya yi alkwarin karewa da kuma mutunta dokokin kundin tsarin mulkin kasar.
Damiba dai ya sanya kakin soji tare da kifa wata jar-hula, sannan ya yafa wani gwado mai dauke da launin tutar kasar ta Burkina Faso.
An dai bai wa kafafen yada labarai damar halartar bikin rantsuwar domin daukar rahoto, amma babu wani bako daga ketare da ya halarci bikin wanda aka gudanar a wani karamin daki da ke ofishin kwamtin fasalta kundin tsarin mulkin kasar.
A ranar 24 ga watan Janairu ne, Damiba mai shekaru 41 ya jagoranci wasu fusatattun sojoji har suka kawar da shugaba Kabore daga kujerarsa bayan al’ummar kasar sun yi ta korafi kan sakacinsa wajen yaki da masu ikirarin jihadi a kasar.
Burkina Faso dai na cikin kasashe mafiya fama da takauci a duniya, kuma tana cikin masu fama da ayyukan ta’addanci a Afrika.
A wani labarin na daban ‘Yan bindiga a Jihar Zamfara da ke Najeriya, sun hallaka mutane 33 a Nasarawar Mai Fara ta karamar hukumar Tsafe da ‘Yar Katsina da ke karamar hukumar Bungudu da kuma Nasarawa a karamar hukumar Bakura saboda abin da aka bayyana a matsayin gaza biyan harajin Naira miliyan 40 da barayin suka dora musu.
Majiyar ta ce kungiyar Ade Aleru, daya daga cikin manyan ‘yan bindiga da suka addabi jihar, ta sanya musu harajin, wanda suka gaza biya.
Wani mazaunin Tsafe, Abubakar Balarabe dake aiki da Gidan Rediyo Thunder Blowers ya ce ya zuwa yammacin jiya, an tabbatar da mutuwar mutane 20.
A yankin Bakura kuma, wani jami’in kula da lafiya, Masud Kyambarawa ya ce an kashe mutane 3, cikin su har da limamin garin, Akilu Dan Malam.
Kyambarawa ya ce lokacin da aka fara harbe harbe, suna garin, inda suka je sa ido, abin da ya sa suka tsere zuwa kauyen Rabah dake Jihar Sokoto.
Jami’in ya bayyana halin da ake ciki a yankin a matsayin abin takaici, lura da yadda mata da yara ke gudu cikin daji domin tsira da rayukan su.
Jaridar ta ce ‘yan bindigar sun hana mutane kauyen ‘Yar Katsina zuwa Sallar juma’a, inda suka tarwatsa su a Masallaci lokacin da suka isa garin, abin da yayi sanadiyar kashe mutane 10.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto Mohammed Shehu, ya ce zai bincika kafin tabbatar da aukuwar lamarin.