Damascus ya sanar da alkaluman kididdigar da girgizar kasar ta shafa a hukumance
Mataimakin ministan lafiya na kasar Siriya Ahmed Zamirieh ya sanar da sabbin alkaluman mutanen da girgizar kasar ta shafa a yankunan dake karkashin ikon birnin Damascus.
Ma’aikatar lafiya ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Adadin wadanda girgizar kasar ta shafa ya kai 403 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai 1,284. Majiyar lardin Aleppo na kasar Siriya a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran kasar SANA ta bayar da rahoton cewa, adadin mutanen da girgizar kasar ta shafa a lardin Aleppo ya karu zuwa 156 sannan adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 507.
Har ila yau, wannan majiyar ta kara da cewa, bayan girgizar kasa mai karfin awo 7.8, an lalata gine-gine 46 a Aleppo kadai.
Girgizar kasa mai karfin maki 7.8 a ma’aunin Richter da ke tsakiyar kasar Turkiyya ta afku a yankuna da dama na yankin yammacin Asiya da kuma yankin Gabashin Bahar Rum da safiyar yau.
Bayanai daga cibiyoyin binciken girgizar kasa sun nuna cewa, wannan girgizar kasa ta afku a kan iyakar Turkiyya da Siriya da tazarar kilomita 26 daga arewa maso gabashin Gaziantep na Turkiyya.
Rahotanni sun nuna cewa an yi rajistar wannan girgizar kasa a kasashen Turkiyya, Siriya, Lebanon, Falasdinu, Iraqi, Jordan, Masar, Saudiyya da wasu sassan Ukraine da Turai da suka hada da Girka, Bulgaria da…
Bayan wannan girgizar kasa, shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya gudanar da wani taron gaggawa tare da halartar mambobin majalisar ministocin kasar domin duba irin barnar da aka yi wa kasar da kuma asarar rayuka da kuma daukar matakan da suka dace dangane da ita.
Har ila yau ma’aikatar tsaron kasar ta Siriya ta tattara dukkanin sassanta, kungiyoyi da cibiyoyinta na dukkanin lardunan kasar domin neman agajin gaggawa ga al’ummar kasar Siriya da kuma neman fitar da wadanda abin ya shafa daga karkashin baraguzan gine-gine da kuma taimakawa wadanda suka jikkata da kuma kawar da tarkace.