A Asabar din nan Ukraine ta ce dakarun Rasha sun fara barin yankunan arewacin kasar a kusa da iyaka da babba birnin kasar Kyiv da birnin Chernigiv, a yayin da kungiyar agaji ta Red Cross suke wani shirin fara kwashe fararen huka daga birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa.
Ukraine ta ce dakarun Rasha ana mayar da hankali ne a yankunan kudanci da arewacin kasar, kwana guda bayan Ukraine ta ce dakarun Rasha ana mayar da hankali ne a yankunan kudanci da arewacin kasar, kwana guda bayan da dubban mutane suka samu ficewa daga Mariupol da saurn yankuna a cikin ayarin motocin bas bas da sauran motoci.
Wani mai bai wa shugaban kasar Ukraine shawara Mykhaylo Podolyak ya ce Rasha ta mayar da hankali a kan wani sabon salo ne a mamayarta yanzu.
Ya ce a yayin da alamu ke nuna dakarun Rasha na ficewa daga biranen Kyiv da Cherngiv, aniyarsu dai ita ce su karbe cikakken iko da yankunan da suka mamaye, don su zauna su kara karfi.
Podolyak ya ce lallai dakarun Ukraine za su bi su yanunan, su kuma kafa tsarin tsaron sama, kuma su kasance masu iko a wurin.
Mariupol ya kasance wani mahimmi birni na Ukraine da ya sha luguden wuta daga Rasha, inda rhotanni ke cewa an kashe mazauna yankin dubu 5.
A wani labari na daban Hukumar kwallon kafa ta Masar ta shigar da kara a hukumance kan Senegal inda ta ce jami’ai da ‘yan wasanta sun fuskanci cin zarafin wariyar launin fata da kuma firgitarwa a lokacin da suke shirin buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a ranar lahadi.
Zalika an rika jifan ‘yan wasan na Masar da kwalabe da duwatsu a lokacin da suke gudanar atasaye gabanin fara fafatawar da suka yi da takwarorinsu na Senegal.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, “An kai wa motocin bas din tawagar Masar hari, wanda ya yi sanadin farfasa tagoginsu tare da jikkata wasu mutane, abinda ya sanya su shigar da kara gaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF da kuma hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.