Sabon kocin Tottenham Antonio Conte ya fara jagorantar kungiyar da kafar dama, bayan da ya samu nasara kan Vitesse da kwallaye 3-2 a wasan farko da kungiyar ta fafata a karkashinsa na gasar Europa a daren ranar Alhamis.
A mintuna 45 na farkon wasan na daren Alhamis da suka fafata sai da magoya bayan Tottenham suka yi tsayuwar ban girma ga Conte ganin yadda cikin mintuna 28 kungiyar tasa dake wasa a gida ta samu nasarar jefa kwallaye 3 a ragar Vitesse.
A shekarar 2016 dai Antonio Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar Chelsea, daga bisani kuma ya samu nasara lashe wasanni 13 a jere, wanda kuma a waccan lokacin kungiyar ta Tottenham ad a yanzu yake horaswa ce ta kawo karshen nasarorin da ya jera da kwallaye 2-0.
A wani labarin na daban kuma hukumar gudanarwar kungiyar Arsenal ta soma nazarin kulla yarjejeniya da tsohon mai horas da Chelsea da Inter Milan Antonio Conte domin maye gurbin kocinta na yanzu Mikel Arteta.
A baya bayan nan Jaridar UK Telegraph ta ruwaito cewa yanzu haka wasanni 5 kacal suka ragewa Arteta don ceton aikinsa na horas da Arsenal, kuma Antonio Conte tsohon kocin Inter Milan da Chelsea ke kan gaba tsakanin wadanda za su iya karbar jagorancin kungiyar ta Gunners.
A watannin baya ne dai aka rika alakanta Conte dan kasar Italiya da komawa gasar Firimiya don horas da kungiyar Tottenham Hotspur, amma yarjejeniyar ta gaza kulluwa.
Kididdiga ta nuna cewa Conte ya samu nasarar lashe wasanni 51 daga cikin 76 da ya jagoranci Chelsea a gasar Firimiya, zalika a karkashinsa ta lashe kofin kakar shekarar 2016 da 2017, kungiyar ta sallame shi a 2018.