Rikici tsakanin kungiyoyin da ke dauke da makamai ya yi sanadin mutuwar mutane 6 a gabashin Jamhuriya Dimokaradiyyar Congo, ‘yan kwanaki bayan kammala tattaunawar lalubo zaman lafiya a zagayen farko, a cewar majiyoyi daga yankin, da kuma masu bincike.
An bai wa hammata iska a ranar Asabar a yankin Fizi dake kudancin lardin Kivu inda kungiyoyi daga Banyamulenge da kuma al’ummar Tutsi ta Congo suka gwabza da mayakan nan ta Biloze Bishambuke.
Dinbim kungiyoyin ‘yan tawaye ne ke aiki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da dama daga cikin sun samo asali ne daga yake yaken basasa da aka yi 25 da suka wuce.
Wani jami’i a yankin ya ce kungiyar Biloze Bishambuke ta mayar da martini ne ga abin da ta kira tsokana daga kungiyoyi 3 daga Banyaamulenge, wadanda ta zarga da kwace wasu kaauyuka 2.
A wani labarin na daban Kungiyar agaji ta Red Cross ta nuna damuwa kan yadda Asibitoci a lardin Kivu ta Arewa mai fama da rikici suka cika makel da mutanen da harbi ya jikkata bayan mummunar zanga-zangar adawa da kasancewar Majalisar Dinkin Duniya da ake ganin ta gaza wajen dakatar da kisan fararen hula a yankin na Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.
Tun ranar biyar ga watan nan na Afrelu aka fara gudanar da zanga-zangar da yajin aiki a arewacin Kivi, domin nuna adawa da tawagar Majalisar Dinkin Duniya, sakamakon yadda kungiyoyin masu dauke da makamai ke cikin karensu babu babbaka wajen aikata kisan gilla, zanga-zangar da yayi sanadin mutuwar mutane 10.
Fiye da mutane 120 da suka ji rauni suna jinya a asibitoci a babban biranen Goma da Beni dake arewacin Kivu da taimakon kungiyar agaji ta Red Cross.