Shi kuwa Putin ya bayyanawa takwaran nasa na Sin dalilan da suka sa ya bada umarnin kaddamar da yaki kan Ukraine, da kuma yadda NATO da Amurka suka dade suna yin watsi da bukatun tsaron Rasha.
Sai dai cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin Rasha da ke Kremlin a Juma’ar nan, ta ce shugaba Vladimir Putin a shirye ya ke ya aika da tawaga zuwa Belarus domin tattaunawa da Ukraine, a dai dai lokacin da sojojin Rasha suka tunkari birnin Kyiv bayan shiga rana ta biyu da kaddamar da yaki kan Ukraine.
China dai na ci gaba da yin taka tsan-tsan kan yakin na makwaftan biyu, inda ta ki bayyana matakin Rasha na afkawa Ukraine a matsayin kare kai.
Bayan makwannin da kasashe suka shafe suna yunkurin shiga tsakani ta fuskar diflomasiya don hana Rasha mamaye Ukraine, daga karshe dai matakan tattaunawar bai hana shugaba Vladmir Putin kaddamar da farmakin soja kan makwafciyar tasu ba, wadda aka afkawa da hare-hare ta sama da kasa.
A wani labarin na daban Russia da China sun chachaki Amurka game da irin mummunar rawar da ta ke takawa a Turai da yankin Asia wanda hakan ke kara rura wutar rashin jituwa a tsakanin yankunan biyu.
Putin da Xi dai sun yi tattaunawar ne yayin da ake gab da bude gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsale wato Olympics na Hunturu, yayin da dukkanin kasashen biyu ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga Amurkar.
A wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen biyu suka fitar, sun yi watsi da yadda Amurka ke ci gaba da aike wa NATO dakarunta sama da dubu dari don shirin ko ta kwana game da kudurin Russia na mamaye Ukraine.
A cewar Russia a yanzu babban abin da ta ke bukata shine samun tabbaci daga NATO kan cewa ba za ta karbi duk wata tawagar dakaru daga Amurka ba, wanda hakan shine kawai hanyar dawo da zaman lafiya a yankin.
Baya ga hakan, Rusha ta kuma ce tana bukatar NATO ta ja kunnen Amurka game da kafa sansanin soji a duk wata kasa dake mamba a tsohuwar tarayyar Soviet, yin hakan a cewarta takalar fada ne kuma babu makawa zata mayar da zazzafan martani.