Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kasashen China, Russia da Serbia da ci gaba da baiwa ‘yan tawayen kasar Myanmar muggan makaman da suke amfani da su wajen hallakawa da kuma azabtar da farafen hula.
A cewar wakilin Majalisar dinkin duniya kan kare hakkin dan Adam a kasar ta Myanmar Tom Andrew, kasashen uku wadanda dukkanin su mambobin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniyar ne sun fara baiwa ‘yan tawayen Myanmar din makaman ne tun watan Fabrairun bara da aka hambarar da gwamnatin kasar.
A don haka Tom Andrew ya bukaci kwamitin tsaron da ya yi gaggawar jan hankulan wadannan kasashe don magance matsalar, da kuma kawo karshen yawon makamai a hannun farafen hula.
Wannan dai na cikin rahoton binciken da aka dade ana jira gada gareshi, kan inda sojojin ke samun makamai, wanda kuma ya bankado yadda bayan sojoji har ‘yan tawayen ke samun makaman.
A cewar sa dukannin kasashen Uku na baiwa ‘yan tawayen makaman ne da cikakken sanin cewa zasu yi amfani da su ne kan fararen hula, wanda kuma hakan take dokokin kasa da kasa ne.
Tun daya ga watan Fabrarirun bara, lokacin da sojoji suka hambarar da gwammnatin Aung San Su kyi ne kasar ta fada cikin mummunan tashin hankalin da ya tafi da rayukan mutane sama da dubu 1 da dari 5, yayin da ake tsare da fiye da dubu 12, sai sama da dubu 44 da suka bar muhallan su ala tilas.
A wani labarin na daban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da shirin musayar mukaman shugabancin ta yadda wadanda ke arewa zasu koma kudu, yayin da wadanda ke kudu zasu koma arewa.A karkashin wannan tsari, shugaban Jam’iyyar zai koma bangaren arewacin kasar, bayan kamala wa’adin shugabancin John Odigun da Adams Ohiomhole, yayin da kujerar Sakataren Jam’iyar zai koma kudancin kasar.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai da shugaban gwamnaonin APC Atiku Bagudu suka bayyana wannan sabon tsarin bayan wani taron da suka gudanar tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa dake Abuja.
El Rufai yace taron na su wanda ya kunshi daukacin gwamnonin jam’iyyar ta su da shugaban kasa ya amince a mayar da daukacin kujerun dake arewacin Najeriya zuwa kudu, yayin da na kudu kuma zasu koma a rewa.
Gwamnan yace a karkashin wannan tsari, zasu koma shiyoyin su domin fasalta yadda zasu raba mukaman yadda kowanne bangaren na kasar zai samu wani mukami.
Ana saran jam’iyyar ta gudanar da tarukkan shiya da kuma na kasa a watan gobe.
Wannan taro bai ce komai ba dangane da inda shugaban kasa zai fito amma ga alama, yana iya komawa kudancin Najeriya tunda jam’iyyar ta kai kujerar shugabancin ta zuwa arewa.