Akalla Mutane kusan 2,000 suka shiga zanga zangar da akayi a kasar Chadi domin nuna goyan bayan sojin kasar da kuma kasar Faransa wadda ta taimakawa kasar tabbatar da zaman lafiya.
Masu zanga zangar na dauke da rubuce rubucen dake bayyana goyan bayan Faransa saboda abinda suka kira taimakawa Chadi.
Mahmoud Ali Seid, ministan matasa da wasanni, wanda kuma yake jagorancin kungiyar CASAC ya bayyana gwamnatin sojin a matsayin wanda ta taimaka wajen tabbatar da tsaro a kasar, yayin da yace suna adawa da masu kona tutar abokan tafiyar su, bayan ya godewa kasar Faransa saboda taimakon da take musu.
A ranar 26 ga watan Fabarairu, Yan adawa a kasar sun gudanar da irin wannan zanga zangar inda matasa suka ja tutar Faransa a kasa, yayin da wasu kuma suka daga tutar Rasha da Chadi tare.
Gwamnatin Chadi tayi alkawarin shirya taron kasa domin shatawa kasar makoma, amma har ya zuwa yanzu ba’a samu gudanar da taron ba.
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Mali ta musanta zargin da ake yi wa sojojinta na yi wa fararen hula da dama kisan gilla a yankin tsakiyar kasar a farkon watan Maris.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta a wannan makon, ya nuna gawarwakin mutane da dama da aka kone su, bayan rufe musu idanu tare da daure hannayensu wuri guda. Wasu daga cikinsu kuma an ga ramuka a bayan kawunansu.
Wani jami’i a a yankin na tsakiyar kasar Mali, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an gano gawarwakin ne a daren ranar Talatar da ta gabata, kuma ana kyautata zaton sune wadanda sojojin Mali suka kama wasu a ranar 20 ga watan Fabrairu, wasu kuma a ranar 1 ga watan Maris.
Sai dai, gwamnati kasar ta yi fatali da zargin, tare da bayyana shi a matsayin karya tsagwaronta.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta sha zargin sojojin Mali da kashe fararen hula da kuma wadanda ake zargin mayakan sa kai ne a tsawon shekaru goma da suka shafe suna yaki da kungiyoyin da ke da alaka da Al Qaeda da kuma IS.