Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar wakilan kasar daidaita kasafin kudi na matsakaicin zango don samar da Naira tiriliyan 4 da nufin sanya su a bangaren tallafin man fetur.
A cewar shugaban Najeriyar an ware Naira biliyan 442 ne kawai don tallafin man fetur a kasafin kudin shekarar bana ta 2022 daga Janairu zuwa Yuni, amma saboda tashin farashin danyen mai, da kuma dakatar da shirin cire tallafin man kwata kwata, kasar za ta bukaci karin Naira tiriliyan 3 da biliyan 557 domin ci gaba da biyan tallafin.
A ranar 24 ga watan Janairun da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta bayyana dakatar da shirinta na cire tallafin man fetur a shekarar bana ta 2022, matakin da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya ce ba zai dore ba.
A wani labarin na daban Sojojin Burkina Faso Akalla 12, da kuma wasu jami’an tsaron sa-kai 4 ne suka rasa rayukan su, sakamakon wani hari da ‘yan ta’adda suka kai musu, a jiya Juma’a.
Arewacin Burkina Faso dai ya rikide zuwa cibiyar hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi wadanda suka fara kai hare-haren cikin kasar daga makwabciyar ta Mali a shekarar 2015.
Alkaluman baya bayan nan kuma sun nuna cewar, zuwa yanzu tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 2,000, tare da raba wasu kusan miliyan 2 da muhallansu.
Tun cikin watan Janairun da ya gabata, Burkina Faso ta kasance a karkashin mulkin soja da Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ke jagoranta, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi saboda gazawar zababben shugaban kasar, Roch Marc Christian Kabore wajen murkushe matsalar ta’addanci.