Buhari Kasar Shugaban Najeriya ya karbi wayar Recep Erdogan shugaban kasar turkiyya a ranar Alhamis.
Shugaban Turkiyya ya na neman goyon bayan Muhammadu Buhari.
Erdogan ya na cikin masu sukar abin da ke faruwa da Falastinawa Jaridar The Cable ta ce shugaban kasar Turkiyya ya kira Mai girma Muhammadu Buhari, ya na neman Najeriya ta taimaka wa kasar Falastina da goyon baya.
Majiyar ta ce Recep Erdogan ya fada wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari cewa ya na sa ran kasarsa ta nuna goyon bayanta ga mutanen kasar Falasdina.
Recep Erdogan ya yi wannan kira ne bayan hare-haren da kasar Israila ta kai wa Jerusalem da Gaza a lokacin da ya zanta da shugaban Najeriya a ranar Alhamis.
Fadar shugaban kasar Turkiyya ta bayyana wannan ne a shafinta na @trpresidency a dandalin Twitter. Sakon ya ce: “Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi waya da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.”
Shugaban Turkiyyan ya sanar da Muhammadu Buhari cewa ya na neman goyon bayan kasashen Duniya domin su yaki zalunci da rashin adalcin kasar Israila.
Kafin ya bijiro masa da maganar halin da kasar Falastina ta ke ciki, Erdogan ya yi wa shugaban Najeriya gaisuwar bikin sallah da musulman Duniya su ke yi.
Erdogan ya nuna cewa ya na sa ran Najeriya za ta goyi bayan Falastinawa kan cin kashin da ake yi masu.
Muhammadu Buhari da Shugaban Turkiyya Source: Facebook Shugaba Erdogan ya tuntubi sauran shugabannin Duniya, daga ciki akwai: Sadyr Japarov na Kyrgyzstan da takwaransa na Afghanistan watau Ashraf Ghani.
Bayan haka Erdogan ya yi magana da shugaban Iraki, Mustafa Al-Kadhimi, tsohon shugaban kasar Malaysia, Mahathir Mohamad da Firayin Minista, Abdul Dbeibeh.
A yau ne mu ka ji cewa wasu majiyoyi masu tushe sun yi watsi da rade-radin cewa tsohon shugaban kasa a mulkin soja,
Ibrahim Badamasi Babangida ya mutu. Majiyoyin sun tabbatar da cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, yana nan cikin koshin lafiya, bayan an yi ta yada cewa ya mutu ana bikin karamar idi.