Masu aikin ceto a Brazil na cigaba da neman masu sauran rai cikin laka da baraguzan gine-gine, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa, da zabtarewar kasa a birnin Petropolis, a daidai lokacin da kawo yanzu adadin wadanda suka mutu a iftila’in ya karu zuwa mutane 117
Har yanzu dai jami’an ceto na lalauben gwamman mutanen da suka bace, yayin da kuma ake fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu.
Guguwar dai ita ce ta baya bayan nan da ta afkawa Brazil cikin watanni ukun da suka gabata, masifun da masana suka ce sauyin yanayi ne ke kara ta’azzara su.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta Petropolis ta ce an ceto akalla mutane 24 da ransu.
Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Taklatar nan.
Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.
A wani labarinna daban rahotanni daga Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan hukumar kula da yawan al’umma ta kasa wato NPC, Malam Zakari Umaru-Kigbu.
Bayanai sun ce lamarin ya auku ne da safiyar Lahadin nan a karamar hukumar Lafiya dake jihar Nasarawa, inda bayan kashe tsohon Kwamishinan, ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ‘ya’yansa mata biyu.
Wani dan ‘uwan marigayin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar al’amarin ga jaridar Daily Trust a Najeriya.
Wasu majiyoyin kuma sun ce ‘yan ta’addan sun nemi a biya su naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin sako mata biyun da suka sace.