Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya gana da Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohamed bin Salman a wata ziyarar kokarin wadata Turai da man fetur da jagoran na London ya ke yi a kasar, irinta ta farko tun bayan tsanantar rikicin Riyadh da turawan yamma biyo bayan kisan dan jarida Jamal Kashoggi.
Ziyarar ta Boris Johnson ita ce irinta ta farko da wani shugaba daga Turai ya kai kasar jagorar larabawa tun bayan kisan Jamal Kashoggi a shekarar 2018, kisan da aka dora alhakinsa kan Mohamed bin Salman ko kuma MBS.
Bayan kammala ganawar jagororin biyu, Boris Johnson ya shaidawa jaridun Birtaniya cewa ya yi tattaunawa mai armashi tsakaninsa da MBS kan yadda Saudiya za ta yi kokari wajen hana katsewar makamashi a Turai da kuma taimawa wajen warware rikicin Ukraine.
A cewar Johnson sun kulla yarjeniyoyi masu muhimmanci a ziyarar, wadanda za su taimakawa ba kadai Birataniya ba har ma da sauran kasashen duniya da kuma ceto kasuwar man fetur daga rikicewar farashi.
Birtaniya na son Saudiya ta kara yawan man da ta ke fitarwa kasuwannin Duniya don dakile barazanar karancinsa saboda rashin mai daga Rasha wanda tuni ya fara haddasa gagarumar matsala musamman ga kasashen Turai.
Boris Johnson ya koka da yadda farashin man ya tashi daga dala 100 kan duk ganga guda kafin fara yakin Rasha a Ukraine zuwa dala 120 a yanzu.