Kamun da ‘yan sandar filin sauka da tashin jiragen saman Heathrow na birnin London na kasar Birtaniya su ka yi wa shugaban hukumar leken asirin kasar Rwanda Janar Emmanuel Karenzi Karake, dake kan sammacin kungiyar tarayyar Turai ya haifar kakkausar suka daga gwamnatin Kigali
Shi dai Janar Emmanuel Karenzi Karake, dan shekaru 54 a duniya a ranar assabar da ta gabata ne ‘yan sandan Interpol na kasar Birtaniya suka kama shi da misalin karfe 9h45 na safiyar ranar assabar da ta gabata a filin sauka da tashin jiragen saman Heathrow dake birnin London, kamar yadda kakakin hukumar yan sanda ta Scotland Yard ya sanar.
Ya kuma kara da cewa, an kama shi ne karkashin sammacin da Kungiyar Tarayyar Turai, ta hannun mahukumtan kasar Spain ta gabatar ne, dangane da zarginsa da aikata laifukan yaki kan fararen hula a kasar Rwanda.
Sai dai kuma wata majiyar shara’a daga birnin Madrid na Spain ta ce, a halin yanzu ba a tuhumar Janar Karenzi Karake kan zargin aikata laifukan yaki, ana zargin sa ne, a kan ayyukan ta’addanci.
Tuni dai ministan harakokin wajen kasar ta Rwanda Uwargida Louise Mushikiwabo ta rubuta rashin amincewar kasarta da kamu na kasar na kasar Birtaniya a shafinta na twitter.
A nasa bangaren ministan shara’ar kasar ta Rwanda Busingye Johnston ya soke wata ziyarar aiki da yayi niyar kaiwa a kasar Spain, inda ya yi niyar ganawa da takwaransa Rafael Catala, kamar yadda majiyar hukumomin Spain ta sanar.
Tun shekara ta 2008 kotun kasar Spain ke bincike kan aikata laifukan yaki, da na kisan kare dangi, tare da ta’addanci da aka aikata a Rwanda, inda a karkashin haka ta bada sammacin kama mata manyan jami’an gwamnatin Rwanda 40 da suka hada da Janar Emmanuel Karenzi Karake.
A wani labarin na daban yau Litinin ake bude taron shekara-shekara da ke hada shugabannin kamfanoni da masu masana’antu daga sassa daban – daban na nihiyar Afirka a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.Taron wanda ake kira ‘’Africa CEO Forum’’, shi ne mafi girma da ke hada shugabannin kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a lamurran siyasa ta tattalin arziki a Afirka.
Taron na bana dai na samun halartar shugabannin kamfanoni da masana’atu sama da 800 daga kasashe 70 mafi yawansu na Afirka sai kuma wasu daga sauran sassa na duniya.
Bayan ga ‘yan kasuwa daga fannoni daban daban, taron na yini biyu kamar dai yadda jadawalinsa ke nunawa, zai kuma samu halartar shugabannin kasashe da na gwamnatoci da dama daga Afirka, da suka hada da shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara mai masaukin baki, Macky Sall na Senegal da ke matsayin shugaban Tarayyar Afirka da kuma shugaban Ghana Nana-Akuffo Ado da ke rike shugabancin kungiyar Ecowas.
An dai gayyato masana da dama ta fannin tattalin arziki musamman daga Bankin Duniya, Bankin Raya Kasashen Afirka da sauran cibiyoyi na kudade, don gabatar da jawabai da ke fayyace irin damarmakin da ke da akwai wajen gudanar da kasuwanci cikin sauki sauki a nahiyar, tare da yin tsokaci dangane da irin kalubalen da ake fuskanta sakamakon matsalaloli na yau da kullum da ke faruwa a duniya.