Wasu da ake zargin mayakan ‘yan ta’adda ne masu ikirarin jihadi, sun kashe mutane akalla 10, a wani harin bindiga da suka kai a wani filin hakar zinare da ke arewacin kasar Burkina Faso.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP ta wayar tarho cewa adadin wadanda suka mutu a harin bindiga din ya kai 14 bayan da aka samu karin wadanda suka mutu sakamakon raunukan da suka samu, inda ya kara da cewa, mutane shida da aka bayar da rahoton bacewar su sun bayyana da safiyar jiya Juma’a.
Fiye da mutane 2,000 ne suka mutu yayin da wasu miliyan 1 da dubu 700 suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ta’addanci da bindiga a Burkina Faso tun daga shekarar 2015, kamar yadda wani kiyasi na kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna.
A wani labari na daban Rundunar Sojin Faransa tace dakarun Burkina Faso da taimakon su sun kashe ‘Yan ta’adda kusan 60 a wata arangamar da suka yi a yankin.
Kasar Burkina Faso na fuskantar barazanar ‘Yan ta’adda tun daga shekarar 2015 lokacin da mayakan dake da alaka da kungiyar Al Qaeda da IS suka fara tsallaka iyaka daga Mali suna kai musu hari.
Kamfanin dillancin labaran Faransa yace mutane sama da 2,000 suka yi asarar rayukan su sakamakon irin wadannan hare hare a cikin kasar.
Hukumar agajin gaggawa a Burkina tace mutane sama da miliyan guda da rabi suka rasa matsugunin su sakamakon tashin hankalin, kuma kashi biyu bisa uku daga cikin su yara ne kanana.
A ranar 14 ga watan Nuwambar bara, wata tawagar ‘Yan ta’adda dauke da daruruwan mutane ta kai hari Inata dake iyakar Mali inda ta kashe mutane 57, cikin su harda jandarmomi 53.
A ranar 23 ga watan Disamba, mutane 41 aka kashe lokacin da ‘Yan ta’addan suka kai hari akan tawagar Yan kasuwa kusa da Ouahigouya kusa da iyakar Malin.