A rahotannin safiya da kafar sadarwa mallakin ingila ta wallafa ya nuna yadda shugaban kasar amurka joe biden yake gudanar da ziyarar bazatan sa a yankin gabas ta tsakiya.
Tafiyar ta biden wacce take zuwa a dai dai lokacin da nahiyar turai ke cikin matsanancin halin matsin tattalin arziki, an ganin shuaban ya shirya wannan ziyarar ne domin samarwa da kasar sa mafita daga halin da take fada sakamakon yakin Ukraine da Rasha.
Farashin man fetur dai yayi tashin gwauron zabi tun fara yakin Rasha da Ukraine din, a dai dai lokacin da kuma kungiyar gmayyar kasashen turai ta sanya takunkuman tattalin arziki kan Rasha wacce ke samar da kaso mafi yawa na iskar gas din da kasashen turai ke amfani dashi wanda hakan ya kara ta’azzara abubuwa a nahiyar turai da Amurka.
Matakan da turai ta dauka ya sanya Rasha ma kakaba takunkumai a kan wasu bangarorin tattalin arziki na Amurka wanda wannan mataki ya matukar sanya amurkawa cikin matsanacin hali.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Joe Biden yayi duk kokarin da zaiyi domin tattaunawa da Saudiyya ta hanyar wayar tarho a kokarin sa na lallabar saudiyyan ta kara adadin man fetur din da take fitarwa a kullum domin samun saukin farashin man fetur a kasauwr duniya ko Amurka ta samu saukin radadin yanayin amma lamarin yaci tura, domin shugabannin saudiyyan sunki sauraran Joe Biden.
A wani salo na samar da mafita a kasar sa Shugaba Joe Biden ya tattaka zuwa gabas ta tsakiya inda ya fara biyawa ta gabar tekun jodan, bangaren da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye.
Shugaban ya bayyana fatan sa na samar da kasashe biyu, ma’ana Isra’ila da Falasdinu kamar yadda yake mafarkin hakan ya faru a gabas ta tsakiya.
Masu sharhin lamurra suna ganin dai babban makasudin tafiyar ta shugaban amurkan bai rasa nasaba da samar da mafita ga amurkan ta hanyar takura saudiyya ta fitar da danyen mai da yawa kasuwar duniya domin farashin man ya sauko.