Shugaban Amurka Joe Biden ya tsaya kan bakarsa cewa, dole ne a kawar da takwaransa na Rasha Vladmir Putin daga kujerar mulki, amma a cewarsa, wannan ra’ayinsa ne na kashin-kansa ba tsarin Amurka ba.
Biden ya ce, ba zai bayar da hakuri ba kan abin da ya furta na ra’ayin kansa.
A karshen makon da ya gabata ne, e Biden ya ce babu yadda za’ayi Putin ya ci gaba da zama a karagar mulki sakamakon mamayar da ya yiwa Ukraine, yayin da ya bayyana mamayar a matsayin shirin kasar da ya kasa haifar da ‘da mai ido.
Biden wanda yake jawabi a birnin Warsaw ya danganta jajircewar kasar Ukraine dangane da mamayar Rasha ta kai musu kamar bijirewa mulkin Tarayyar Soviet lokacin neman ‘yanci, yayin da ya bayyana cewar ya dace duniya ta shirya fuskantar rikici na dogon lokaci nan gaba.
Shugaba Biden ya bayyana wa mutanen Ukraine cewar duniya na tare da su, yayin da ya shaida wa mutanen Rasha cewar ba sune abokan gabar su, saboda haka su zargi shugaba Putin saboda takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kakaba musu.
Shugaban Amurkar ya kuma gargadi Putin da kar ya kuskura yace zai mamaye koda taki guda na wata kasa dake cikin kungiyar NATO, domin kuwa zai gamu da martini mai karfi daga kasashen dake cikin kawancen.