Mai horar da kungiyar kwallon kafar Burkina Faso, Kamou Malo, na ci gaba da samu goyan baya daga yan kasar a wannan tafiya na neman lashe kofin kwallon kafa dake gudana a Kamaru.Kamou Malo wanda baya ga harakokin kwallon kafa aka bayyana cewa dan Sanda ne a Burkina Faso.
Sai dai wani abin lura mai horar da kungiyar kwallon kafar ta Burkina Faso Kamou Malo, baya ga kwallon kafa,yanzu haka yana daga cikin manyan hafsan yan sandar Burkina Faso.
Inda muka dan duba tarihin sa ,ranar 29 ga watan yuli na shekara ta 2019 ne hukumar kwallon kafar Burkina Faso ta cimma yarjejeniya da Kamou Malo na ganin ya karbi ragamar horar da kungiyar ta Burkina Faso.
Tarihi ya nuna cewa ya lashe kofin kasar na kwallon kafa a shekara ta 2012,Kamou Malo na daga cikin masu horar da ake sa ran za su shiga tarihi da kafar dama.