Barazanar Isra’ila Na kashe Jagororin Falasdinu Ba Zai Hana Ci Gaba Da Gwagarmaya Ba.
A cikin wani bayanin da Isra’ila ta wallafa a shafinta na yanar Gizo ta fusata game da bayanann da Shugaban ofishin siyasa na Kungiyar Hamas a gaza yahay sinwar yayi inda ta bayyana shi da ire-irensa a matsayin babban barazana ga makomar gwamnatin isra’ila day a zama waji bi a kawar da su.
A hirara da kamfanin dillancin labarai na press news yayi da Ahmad Al-modellel ya fadi cewa idan dai isra’ila ta taba Yahya sinwar ta saurari gasa tsakanin makamai masu linzami na kungiyar Hamas da JIhadil islami da za ta rika harbawa a tsakiyar Isra’ila, gwamnatin sahyuniya ce ke da alhakin kisan dukkan shuwagabannin gwagwarmaya a yankin Falasdinu.
Haka zalika kungiyar hamas ta yi gargadi cewa duk wani yunkurin kashe Yahya Sinwar ko wani jigo a cikin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu to ta zata fuskanci mayar martani mai tsanin kuma za ta harba makamai masu linzami a dukkan birane da muhimman cibiyoyin Isra’ila.
READ MORE : Ziyarar Shugaban Kasar Siriya A Tehran Bude Wani Sabon Shafin Dangantaka Ne.
HKI ta mamaye yankunan falasdinawa ne tun a shekara ta 1948 da fakewa da daukar fansar kisan kare dangi da aka yi wa yahudawa wato Holucust a kasar Jamus.