Gungun kungiyoyin kare hakkin bil adama samada 230 na Duniya ne suka bukaci da lallai sai shugabar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya wato Mitchell Bachelet ta ajiye mukaminta bisa abinda suka kira rashin iya aikin ta
Samada kungiyoyin fararen hula dake rajin kare hakkkin bil adama 230 ne suka kaddamar da kamfen din kawar da shugabar dagamukamin nata.
Wadda suka bayyana ta da wadda bata iya aiki ba bayaga rashin maida hankali kan abunda ya dace
Daga cikin misalan inji wadannan kungiyoyi harda nuna halin ko in kulak an yan kabilar Urgy, a china dangane da cin kashin da ake musu.
A ziyarar data kai China ma bachelet bat ace komi ba game da halin da musulmin yan kabilar ta Urgui ke ciki, duk kuwa da ta ziyarci yankin yammacin Xinjiang, inda ake zargin China na tsare da Miliyoyin Musulmi yan kabilar ta Urgyui. Bayaga danne hakkin kananan kabilu marasa rinjaye, wadanda ake azabtarwa a kullu yaumin
Tuni dai MDD ta bayyana halin da ake ciki a Xinjing amatsayin kisan kare dangi, da kuma cin zarafin dan adam, zargin da hukumomin china suka sha musantawa.
A wani labarin na daban kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar ce da kuri’u dubu 1271 da masu zabe sama da dubu 2300 suka kwashe dare suna kadawa. Tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi ya zo na biyu da kuri’u 316, sai Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo a matsayi na uku da kuri’u 235 sai kuma shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan da ya samu kuri’u 152.
Rochas Okorocha bai samu kuri’a ko guda ba
Ogbonnaya Onu ya samu kuri’a 1
Sanata Ben Alade ya samu kuri’u 37
Ikeobasi Mokelu bai samu kuri’a ba
Nwajiuba Chukwuemeka ya samu kuri’a 1
Yahaya Bello ya samu kuri’u kuri’u 47
Ahmed Lawan ya samu kuri’u 152
Yemi Osinbajo ya samu kuri’u 235
Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 316
Ahmed Sani kuri’a 4
Dave Umahi ya samu kuri’a 38
Tunde Bakare bai samu kuri’a ko guda ba
Tinubu ya lashe daukacin akwatuna da aka jera kawo yanzu, inda ya samu kuri’u sama da 1000.
Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ke biye da shi.
Yayin da Amaechi ya samu kuri’u 316, Osinbajo ya samu kuri’u 235.
‘Yan takara
‘Yan takara 14 da suka fafata a zaben sun hada da Mista Chukwuemeka Nwajuba, Fasto Tunde Bakare, Mista Ahmed Rufa’i, Sanata Rochas Okorocha, Mista Jack Rich, Gwamna Ben Ayade, Gwamna David Umuahi, Asiwaju Bola Tinubu, Sen. Ahmed Yarima, Dr Ahmed Lawal, mataimakinsa. -Shugaban kasa Yemi Osinbajo, Mista Rotimi Amaechi, Gwamna Yahaya Bello da Mista Ogbonnaya Onu.
Wadanda suka janye
Tun da farko dai mutane tara ne suka janye daga takarar da suka hada da Mrs Uju Kennedy-Ohnenye, Dr Felix Nicholas, tsohon gwamna Godswill Akpabio, tsohon gwamna Ibikunle Amosun, tsohon kakakin majalisar Dimeji Bankole, Sen. Ajayi Boroffice, Gwamna Muhammad Badaru, Sen. Ken Nnamani. da Gwamna Kayode Fayemi.