Har yanzu Arsenal da Barcelona na sha’awar dauko dan wasan gaba nan, Alvaro Morata a karshen wannan kaka, kamar yadda jaridun labarin wasanni da dama suka ruwaito , ciki har da Calciomercato.
Hakan ne ma ya sa Arsenal da Barceloa ke ta fafutukar ganin sun dauko dan wasan, amma kuma babbu wata magana mai karfi ya zuwa yanzu.
Sai dai har yanzu kungiyoyin biyu na dakon ganin ya koma ainihin kungiyarsa din a Spain a karshen wannan kaka.
A wani labarin na daban Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin takwarorinsa na Afirka, a daidai lokacin da alamu ke nuna da cewa Faransa na shirin janye dakarunta da ke yaki da ayyakan ta’addanci daga kasar Mali.
Bayan ganawa da shugabannin kasashen na Afirka, gobe alhamis Macron zai wuce zuwa birnin Brussels domin halartar taron Kungiyar Tarayyar Afiirka ta Tarayyar Turai wanda zai share tsawon kwanaki biyu.
Tun shekara ta 2013 ne dai Faransa ta tura dakarun domin yaki da ayyukan ta’addanci a Mali, to sai dai har yanzu akwai gagarumar fargaba dangane da makomar tsaro a yankin, tare da yiyuwar yaduwa ayyukan ta’addanci zuwa sauran kasashen da ke gabar teku.
Lura da wannan matsala ce, Faransa da sauran kasashen Turai suka yanke shawarar kafa sabuwar runduna mai suna Takuba da za ta maye gurbin Barkhane, shirin da ga alama bai samun goyon bayan sabbin magabantan birnin Bamako ba.