Shugaban na Turkiyya ya tabbatar da cewa Ankara za ta ci gaba da kokarin kawo karshen yakin da wanzar da zaman lafiya ta hanyar adalci bisa shawarwari tare da bayar da goyon baya mai ƙarfi wajen sake gina kasar Ukraine da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Erdogan ya ce shirin hatsi na Bahar Black ya ba da damar wucewar kusan tan miliyan 33 na hatsi don isa ga masu bukata, tare da hana matsalar abinci ta duniya. Hoto: AA
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Ankara za ta ci gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.
“Yayin da muke ci gaba da hadin gwiwa da Ukraine, za mu ci gaba da kokarin kawo ƙarshen yaƙin da wanzar da zaman lafiya cikin adalci bisa shawarwari,” in ji Erdogan a ranar Juma’a a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Ukraine Volodymr Zelenskyy, a Istanbul.
Ya ƙara da cewa “Turkiyya a shirye take ta karɓi baƙuncin taron zaman lafiya wanda ita ma Rasha za ta halarta.”
Ya bayyana cewa, Turkiyya za ta goyi bayan sake gina ƙasar Ukraine da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Turkish President Erdogan:
– We discussed developments on war & navigational safety in Black Sea, including grain deal
– We’ll strongly contribute to reconstruction of Ukraine after war ends
– We agreed to increase our bilateral trade to $10B pic.twitter.com/KENns2Kb1P
— TRT World (@trtworld) March 8, 2024
Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa: “Shigar da yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci (da Ukraine) da wuri-wuri, babu shakka zai farfaɗo da dangantakarmu da ƙarfi.
A yayin taron manema labarai, Shugaban Ƙasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya gode wa Turkiyya da al’ummar Turkiyya bisa goyon bayan da suka bayar ga ‘yancin kan yankin Kiev, da ƴancin kai, yana mai cewa sun samu “sakamakon ayyukan jinƙai.”
I started my meeting with President @RTErdogan.
I am grateful to Türkiye for its reliable support for Ukraine.
Both of our countries, the entire region, and global food security require unconditional security of navigation in the Black Sea. We can accomplish this by working… pic.twitter.com/kV8ms9RIeo
— Volodymyr Zelenskyy / Володимир Зеленський (@ZelenskyyUa) March 8, 2024
Hanyar jigilar hatsi ta Bahar Aswad
Kafin taron na hadin gwiwa, shugabannin biyu sun gana a ofishin Dolmabahce da ke Istanbul.
Zelenskyy ya faɗa a cikin wata sanarwa a farkon taron cewa yana godiya da goyon bayan Ankara.
Ya ce, yana da sha’awar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, da kare zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a Tekun Bahar Aswad, da kuma ganin Ukraine ta yi aiki tare da kamfanonin tsaron Turkiyya.
Ya ƙara da cewa suna kuma bukatar taimakon Turkiyya wajen sako fursunonin yakin Ukraine da kuma “dukkan mutanenmu, ciki har da ‘yan Tatar na Crimea, wadanda Rasha ke riƙe da su.”
DUBA NAN: Gwamnati Zata Daina Hada Hadar Binance
A Istanbul, Zelenskyy kuma zai ziyarci wuraren ajiyar jiragen ruwa inda kamfanonin Turkiyya ke gina wa sojojin ruwa na Ukraine guda biyu, a cewar ofishinsa.