Wasu ‘yan bindiga a Najeriya sun fille kan Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltar al’ummar Gwamna Charles Soludo a majalisar dokokin Anambra da ke yankin Kudu-maso-gabashin kasar.
Mista Okoye, wanda ke wakiltar mazabar Aguata 2 a jihar Anambra, an sace shi ne tare da mai taimaka masa, Cyril Chiegboka, a ranar Lahadin makon jiya a hanyar Aguluzigbo, a karamar hukumar Anaocha ta jihar.
An ce an jefar da kan sa ne a wani wurin shakatawa na Chisco da ke Amichi, a karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar ta anambra a ranar Asabar, kwanaki shida bayan da aka sace shi.
‘Yan sanda sun tabbatar da kisan
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Asabar.
Ya ce daga baya an tsinci gawar dan majalisar a kan titin Ideani, unguwar Nnobi, karamar hukumar Idemili ta Kudu. Sai dai bai bayyana komai kan makomar mai taimaka wa dan majalisar, Cyril Chiegboka ba, amma akwai alamun mai yiwuwa ma an kashe mataimaki.
Abin kunya ga tsaron kasa
Kakakin ‘yan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Echeng Echeng, ya bayyana kisan dan majalisar a matsayin “abin kunya ga tsoron kasa”
Mista Echeng ya kuma jajantawa ‘yan uwa da abokanan dan majalisar tare da ba da tabbacin cewa ‘yan sanda za su zakulo wadanda suka kashe shi.
Wani faifan bidiyo da ya dauki kan da aka jefar a wurin shakatawa ya bazu a shafukan sada zumunta daban-daban.
A wani labarin na daban daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zanga Asabar a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi dangane da abin da suka kira kasancewar Faransa a kasar, wadda suka zarga da taimaka wa sojojin da ke mulkin kasar.
Masu zanga zangar sun kona akalla tutocin tsohuwar uwargijiyar tasu 2, kana suka lalata gidajen mai mallakin kamfanin Total na kasar Faransa, tare da yin awon gaba da wasu kayayyaki a gidajen man.
Zanga zangar da kungiyar farar hular nan ta Wakit Tamma mai hamayya da gwamnatin kasar ta shirya ta samu goyon bayan hukumomi da alama, inda kamfanin dillancin labaran Faransa ta ruwaito cewa ana iya ganin tawagar ‘yan sanda mai karfi da ke tabbatar da cewa ba a wuce gona da iri ba.
A ranar 20 ga watan Afrilu shekarar 2021 ne rundunar sojin kasar Chadi ta sanar da cewa shugaba Idriss Deby Itno ya mutu a fagen daga, yayin fafatawa da ‘yan tawaye, inda a ranar ce aka nada dansa Mahamat Deby a matsayin shugaban kasar.