Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki ya bayar da rahoton cewa, gwamnan lardin Karbala Nasif Jasem Alkhitabi ya sanar da cewa, daga yau Alhamis an rufe dukkanin ma’aikatun gwamnati a birnin Karbala, domin shirin gudanar da tarukan ziyarar arba’in na Imam Hussain (AS).
Ya ci gaba da cewa, kamar yadda aka saba a kowace shekara ana rufe dukkanin ayyuka a ma’aikatun gwamnatia lokacin tarukan arba’in, domin bayar da dama ga tsare-tsare na wannan taruka,a kan haka a wannan karon ma daga yau an rufe dukkanin ma;aikatun gwamnati a lardin na Karbala da ke kudancin Iraki.
Baya ga bangaren ayyukan gwamnati, an dakatar da ayyuka daban-daban wadanda ba su shafi bangaren kiwon lafiya da tsaro da kuma harkokin kasuwancin mutane ba.
A nasu bangaren dakarun sa kai na hashd Shaabi suna cikin masu taimaka ma jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu, kamar yadda kuam suke taimaka wa bangaren ayyukan lafiya da bayar da agajin gaggawa.
A wani labarin na daban tankokin mai da Iran ta aikewa kasar Lebanon sun fara shiga kasar bayan da katafaren jirgin ruwan dakon mai na kasar ta Iran ya sauke kayansa a gabar ruwan Syria.
Rahotanni sun tun a jiya ne Tankokin mai da Iran ta aikewa kasar Lebanon sun fara shiga kasar ta yankin Biqa da ke kan iyaka da Syria, bayan da jirgin dakon mai na farko ya fara sauke man da yake dauke da shi a gabar ruwan ta Baniyas a kasar Syria, ayyin da kuma wasu jiragen suke kan hanya.
Kafin wanann lokacin dai babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah wanda shi ne ya shigo da man ya bayyana cewa, za a rarraba ne a dukkanin yankunan kasar ba tare da la’akari da wani bambanci ba.
Sannan kuma ya jaddada cewa, za a sayar da man ne bayan an karya farashinsa kasa sosai, ta yadda kowa a kasar Lebanon zai iya sayea cikin sauki, kuma tuni Hizbullah da gwamnatin Lebanon sun shiga tattaunawa kan yadda za a kayyade farashin da za a sayar da shi, ta yadda kowa zai iya sayea cikin farashi mafi sauki.