An kashe ‘yan ta’adda 22 a cikin kwanaki biyu a arewacin Siriya da Iraqi
A wani yanayi da ake ci gaba da bayyana ra’ayoyin kasashen duniya game da hare-haren da sojojin Turkiyya suka kai a arewacin Siriya da Iraqi, Ankara ta ba da kididdiga kan hasarar wadannan hare-haren.
A farmakin da sojojin suka kai an kashe mayakan Kurdawa 22 da suka hada da ‘yan PKK 10 a arewacin Iraqi da kuma ‘yan ta’adda 12 na kungiyar “Siriyan Democratic Forces” a arewacin kasar.
Majiyoyin yada labarai sun ce akalla mayakan da fararen hula 125 ne suka mutu ko kuma suka jikkata a hare-haren da jiragen saman Turkiyya suka kai a yankunan Kurdawa da ke arewacin Siriya.
A daidai lokacin da barazanar da Ankara ke yi na kai hari ta kasa a arewacin Siriya ta yi kamari, kafafen yada labarai sun buga hoton isowar kayan sojan Turkiyya a arewacin Siriya.
Read More :
Da Dumi Dumi: Iran Ta Lallasa Wales A Wasan Cin Kofin Duniya Na Qatar.
Ɗan bindiga a Amurka ya harbe mutum 10 a cikin kanti.
Martanin da hukumomin Falasdinawa suka yi kan shahadar wani matashin Bafalasdine.
ikirari na Ukraine; Har yanzu Rasha na kera makamai masu linzami masu cin dogon zango.