An kashe ‘yan jarida takwas a Mexico cikin 2022
Wani sabon rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin dan Adam ta fitar ya nuna an kai ƙololuwa a munanan hare-haren da ake kai wa ‘yan jarida a Mexico, lamarin da ke nuna mummunan matakin da gwamnati ke ɗauka kan ‘yan jaridar.
Rahoton kungiyar da ƙungiyar Article Nineteen ta fitar ya ce a wa’adin farko na gwamnatin Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador, an samu karuwar kai wa ‘yan jarida hari da kashi 85 cikin 100 idan aka kwatanta da zamanin mulkin wanda ya gada.
Wakiliyar BBC ta ce ya nuna wata ukun farko na shekarar nan su ne mafiya muni ga ‘yan jaridar Mexico, inda aka kashe ‘yan jarida takwas.
READ MORE : Iran Ta Zargi Isra’ila Da Kawo Cikas A Yunkurin Kawar Da Makaman Kare Dangi A Gabas Ta Tsakiya.
An kai wa ‘yan jarida hari sau 2,000, ciki har da kisan akalla 33 cikin shekara uku.
Mista Lopez Obrador da gwamnatinsa sun sha cin zarafin ‘yan jarida a lokacin taron manema labarai.
READ MORE : Tunusiya Ta ce; Ba Za ta Amince Da Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidanta Da Kasar Turkiya Ta yi Ba.
READ MORE : Iran Na Maraba Da Fadada Dangantaka Da Kasashen Yankin Musamman Na Tekun Kasfiya.