An kama Wasu Mutane 3 Masu Kai Wa ‘Yan Boko Haram Bindigogi A Tafkin Chadi.
Gamayyar sojojin Nijeriya da na kasashen waje (MNJTF), sun samu nasarar cafke wasu mutum uku da suke safarar makamai zuwa Nijeriya ta iyakokin Kamaru da Najeriya.
Wata majiya ta shaida cewa an cafke mutane guda ukun ne a ranar 28 ga watan Afrilun 2022, bayan da aka tsegumta wasu bayanan sirri da aka samu game da wasu ake zargi suna safaran bindigogi da mkamai zuwa cikin Nijeriya daga Gamborun Ngala, da ke iyakar da ta hada Nijeriya, Kamaru da Nijar.
Wannan ne Yasa sojojin suka kai farmaki inda suka samu nasarar cafke wadanda ake zargin da wannan aika I aika, ya ce makaman da aka kama sun hada da bindiga kirar AK-47 wanda ake shirin ake wa zuwa sansanin ‘yan Boko Haram.
READ MORE : Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Gayyaci Jakadan Kasar Sweden Dake Tehran.
Tuni Sojojin suk yi awun gaba da wadanda suka kama domin kara zurfafa bincike a kansu. Sojojin sun bayyana irin nasarorin da suke samu akokarin da ake na dakile hare-haren ‘yan Boko Haram.
READ MORE : Hamas Ta Jinjinawa Jagora Kan Tallafin Da Take Samu Daga Kasar Iran.
READ MORE : Sudan; Shugaban Kasa Ya Bukaci ‘Yan Adawa Su Ajiye Bambance-Bambance Tsakaninsu Da Gwamnati.