Gwamnatin Amurka ta sanar da haramtawa jami’ai da wasu daidaikun ‘yan Somaliya takardar izinin shiga kasar, inda ta zarge su da raguza tsarin dimokuradiyya kasar tasu.
Zaben wanda aka fara a watan Nuwamban da ya gabata, ya kamata a gudanar da shi ne shekara guda da ta wuce amma aka dakatar da shi sakamakon jinkiri da aka samu da suka hada da rashin cimma matsaya kan yadda za a gudanar da zaben, da kuma rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da firaminista a Somalian.
Ya zuwa yanzu dai, an zabi 179 daga cikin 275 na ‘yan majalisar a Somalia. Kuma ‘yan majalisar ne za su zabi shugaban kasa, amma har yanzu ba a sanya ranar da za a gudanar da zaben na shugaba ba.
A wani labarin na daban Kasashen Turai da kuma wadanda ke makwaftaka da Somalia, sun bayyana fargaba kan takaddamar da ke ta’azzara tsakanin shugaban kasar da kuma Firaminista, inda a yanzu haka jami’an tsaro masu biyayya ga bangarorin da basa ga maciji, ke yin sintiri dauke da muggan makamai a wasu sassan birnin Mogadishu.
A Talatar nan ce dai, sojojin da ke biyayya ga Firaminista Roble suka mamaye wasu wurare a kusa da fadar shugaban kasa, kwana guda bayan da shugaban ya sanar da dakatar da firaministan bisa zarginsa da cin hanci da rashawa, da kuma yin katsalandan a binciken da ake yi kan zarge zarge na kwace wasu filaye, yayin da shi kuma Firaministan ya zargi shugaban da yin zagon kasa ga zaben da ake shirin yi.
Tuni dai masu sa ido na kasa da kasa suka bukaci bangarorin biyu da su sasanta rikicin nasu da ke ci gaba da tabarbarewa yayin da wasu dattijan siyasa da shugabannin gargajiya suka fara kokarin shiga Tsakani.
A gefe guda kuwa, gamayyar ‘yan takarar shugabancin kasar ta Somalia ya bukaci shugaba Mohammed Farmaajo da ya gaggauta ficewa daga ofishinsa tare da yin kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa akan tuhumar da ake masa kan yiwa Firaminista juyin mulki da kuma gurfanar da wadanda suka taimaka masa.
Daga ketare kuwa ofishin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka ya yi gargadi cewa Washington ta shirya daukar mataki kan wadanda ke kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a Somalia.
Dangantaka tsakanin shugabannin kasar ta Somalia ta dade yin tsami, sai dai rikicin na baya bayan nan yafi tayar da hankula a ciki da wajen kasar, ganin yadda lamurra suka rincabe a daidai lokacin da hukumomin Somalian ke shirin gudanar da zabuka da kuma yaki da mayakan kungiyar Al Shebaab.