Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da tallafin Dala biliyan 1 tare da aikewa da makamai masu cin dogon zango da kuma jirage marasa matuka ga Ukraine, yayin da ya jaddada kudirinsu na agaza wa kasar a yakin da take gwabzawa da Rasha.
A yayin sanar da tallafin, shugaba Biden ya ce, kai tsaye za su tura wa Ukraine kayayyakin soji daga Ma’aikatar Tsaron Amurka domin taimaka wa kasar wajen tunkarar Rasha da ta yi mata mamaya.
Kamar dai yadda aka yi zato, shugaban na Amurka bai mayar da hankali kan haramta wa Rasha ratsa sararin samaniyar kasashen yammaci ba, matakin da ita ma Kungiyar Tsaro ta NATO ta ki amincewa da shi saboda gudun kazancewar rikicin.
Ana ganin daukar wannan matakin na harmata wa Rasha ratsa sararin samaniyar, ka iya tilasta wa kasashen NATO yin gaba-da-gaba da Rashar.
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce, Ukraine za ta karbi karin makaman kakkabo jiragen yaki har guda 800 da kuma makaman tarwatsa tankokin yaki guda dubu 900, ba ya ga wasu kananan makamai guda dubu 7 da kuma harsashen bindiga miliyan 20.
A wani labarin na daban Mataimakin Firaministan kasar Ukraine Iryna Vereshchuk, ya ce harin da Rasha ke kaiwa kan Mariupol ya hana aikin kwashe ‘yan gudun hijira daga birnin mai tashar jiragen ruwa na Ukraine.
Bayanai sun ce sojojin Rasha da suka dakatar da wasu motocin bas na mutanen da ke kokarin tserewa daga yankin Kyiv, sun yi wa birnin Mariupol kawanya.
Kawo yanzu fararen hula dubu 1 da 582 suka rasa rayukansu a Ukraine tun bayan farmakin da Rasha ta kai kan kasar.