Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya da jiragen soji masu saukar angula kirar Viper guda 12 a kan kudi kusan da bilyan daya, duk da kokarin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi domin ganin cewa Amurka ta hana wannan ciniki.
Yarjejeniyar cinikin Jiragen na AH-1Z Vipers mai dauke da tsarin hangen nesa ko cikin dare da kuma horo ya kai dalar Amurka miliyan 997.
Amfani da kuraman jirage
Wannan na zuwa ne yayin da mahukuntan Najeriya suka bayyana fara amfani da jirage marasa matuka da aka fi sani da drones a wani yunkuri na kawo karshen ayyukan ta’addanci a Kasar.
Mai taimaka wa shugaban Kasar ta fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan, bayan ganawa ta musamman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin kasar 36 da kuma tsoffin shuwagabannin kasar.
A wani labarin na daban Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce nan ba da jimawa ba ne za ta gabatar wa majalisar dokokin kasar da bukatar neman izinin gayyato sojojin kasashen Yamma domin yaki da ayyukan ta’addanci a cikin kasar.
Wasu ‘Yan kasar na daukar sojojin kasashen waje, wadanda ke aiki tare da sojojin Nijar tamakar “dakarun mamaye”
Ministar harkokin wajen Nijar ya bayyana haka ne yayin ganawa da takwaransa na Jamus da ta kammala ziyarar kwanaki biyu a Nijar, inda suka tattauna da shugaban kasar Mohamed Bazoum a kan huldar kasashen biyu.