Al-Fayyad; Muna Goyon Bayan Warware Rikicin Siyasar Iraqi Ta Hanyar Lumana.
Babban kwamandan dakarun sa kai na Iraqi (PMU) da aka fi sani da Larabci da Hashd al-Sha’abi, ya ce kungiyar da ke yaki da ta’addanci tana goyon bayan warware rikicin kasar a siyasance.
Tashar talabijin ta al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Falih al-Fayyadh yana fadar haka a wani taron manema labarai da ya gudana a babban birnin kasar Bagadaza a yammacin jiya Litinin, PMU ta shawarci dukkanin kungiyoyin siyasa da su warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da mu’amala ta hanyoyin shari’a.
Dakarun “Hashd al-Sha’abi sun yi alkawari ga al’ummar Iraqi cewa za su ci gaba da tafiyar da harkokin siyasa ta hanyar cibiyoyin shari’a tare da jaddada bukatar kariya da kiyaye cibiyoyin dimokiradiyya a kasar,” in ji al-Fayyadh.
Ya kara da cewa dole ne dukkan manyan kungiyoyin siyasa a kasar ta Iraqi su bi kundin tsarin mulkin kasar tare da amincewa da sakamakon zabe.
Fayyadh ya kuma yi kira da a kwantar da hankula da kuma kamun kai a tsakanin dukkanin bangarori domin amfanin kasar Iraqi, yana mai cewa PMU tana jaddada kudurin ta na goyon bayan aiwatar da tsarin siyasa da mika mulki ta hanyar akwatin zabe.