‘Yan tawaye a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kashe sojoji 6 a wani hari da suka kai a kudu maso gabashin kasar inda aka shafe shekaru ana gwabza yakin basasa.
Dan majalisar ya kara da cewar, baya ga sojoji 6 da suka mutu, an kuma kashe mayakan ‘yan tawaye uku.
Fouele ya ce kungiyar mayakan masu fafutukar neman sauyi da aka kafa a watan Disamban shekarar 2020 domin hambarar da shugaba Faustin Archange Touadera, ne suka kai harin.
A wani labarin na daban kuma an dage sauraron shari’ar farko da aka dade ana jira a karkashin kotun da aka kafa domin hukunta laifukan yaki a rikicin da ya tagayyara al’ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Karo na biyu kenan da ake dage lokacin fara sauraron shari’ar a cikin watan Afrilun nan.
Lauyan daya daga cikin wadanda ake tuhuma da aikata laifukan yakin, Paul Yakola, ya shaida wa manema labarai cewa, masu kare wadanda ake tuhuma sun bukaci kotun da ta dage zaman ne saboda rashin cikakken shirin da suka y ikan shari’ar.
Sai dai dan sanda mai shigar da kara Alain Wabibikaye ya ce ya yi imanin hakan wata dabara ce ta jinkirta fara shari’a kan tuhume-tuhumen aikata munanan laifukan yakin da aka dade ana jiran gani.
A ranar 19 ga watan Afrilu aka fara dage zaman sauraron kararrakin, lokacin da lauyoyin wadanda ake kara suka kauracewa zaman kotun.
Shari’ar dai na da alaka da kisan kiyashin da aka yi wa farar hula 46 a kauyukan Koundjili da Lemouna na arewacin kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a watan Mayun shekarar 2019.