Abdullahian; Bai Kamata Kasashen Waje Su Yi Tasiri A Harkokin Tsaron Gabas Ta Tsakiya Ba.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce kasarsa na jaddada tattaunawa da hadin gwiwa a yankin, don haka bai kamata mahukuntan yankin su bar kasashen waje su yi tasiri a hadin gwiwa da kwanciyar hankali a yankin ba.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya tattauna a yammacin yau da ministan harkokin wajen masarautar Oman Badar Al-Busaidi kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Kazalika da wasu batutuwan da suka shafi al’amuran shiyya-shiyya da na kasa da kasa.
Dangane da ziyarar da shugaban kasar Iran ya kai masarautar Oman, ministan harkokin wajen kasarmu ya dauki wannan ziyara a matsayin wani sabon sauyi a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Dangane da kokari na musamman da shugabannin kasashen biyu suka yi na ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin Tehran da Muscat, Amir Abdollahian ya jaddada bukatar bin diddigi da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma yayin wannan ziyara.
Amir Abdullahian ya yi maraba da ziyarar da tawagar gwamnatin Omani ta kai birnin Tehran domin bin diddigin yarjeniyoyin da aka cimma, ya kuma jaddada aniyar bangarorin biyu na ci gaba da yin hadin gwiwa.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Omani Badr al-Busaidi ya jaddada aiwatar da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma yayin ziyarar da Ayatullah Raisi ya kai kasar Oman cikin nasara.
Ministan harkokin wajen kasar Omani ya kuma sanar da kafa wata kungiyar aiki a gwamnatin Omani domin bin diddigin yarjejeniyoyin da aka cimma a ziyarar da shugaban kasarmu ya kai birnin Muscat na baya-bayan nan.